Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISAIAS Na Ci Gaba Da Kadawa A Birane Da Garuruwan Amurka


Guguwar Isaias a New York
Guguwar Isaias a New York

Matsananciyar guguwar nan da aka yi wa lakabi da “ISAIAS” tana kara ketawa a tsakiyar jihar New York da New England bayan ta hanzarta ratsawa a yankin tsakiyar Atlantika na Amurka, inda akalla ta kashe mutum hudu.

Hukumar kula da matsananciyar guguwa ta Kasa ta aika da gargadin guguwa mai karfi daga tsibirin Manasquan Inlet a New Jersey zuwa Stonington, Maine, Long Island da Long Island Sound, da Marta ta Vineyard, Nantucket, da Block Island.

An yi hasashen cewa guguwar “ISAIAS” zata zo da ruwan sama, da iska mai karfi da hadari a wuraren da yawa.

Guguwar “ISAIAS” ta isa bakin tekun Ocean Isle, North Carolina ranar Litinin din data gabata da daddare a matsayin mahaukaciyar guguwa ta daya, kuma ta tashi da sauri a gabar tekun, ta rage karfi amma kuma ta haddasa ambaliya, karyewar bishiyoyi, da kuma katsewar wutar lantarki.

“ISAIAS” ta haifar da wata mahaukaciyar guguwa wacce ta kashe mutum biyu a Windsor, North Carlina.

An kuma bayar da rahoton akwai alamar guguwar a Delaware, Maryland, New Herse, da Virginia. Yara da dama sun sami raunuka lokacin da iska mai karfi ta rushe rufin wata cibiyar kulawa da yara a Philadelphia.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG