Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guguwa Mai Karfi Ta Hallaka Mutane A Birnin Nashville


An samu wata guguwa mai karfi hade da ruwa a birnin Nashville, a Tennessee da wasu wurare a yankin da safiyar yau Talata, inda ta halaka akalla mutane bakwai da kuma yin barna sosai.

Wani bidiyo da aka dauka ya nuna yadda guguwar ta yi ta ratsawa cikin unguwanni, hade da walkiya, inda ta yi ta rushe gine-gine. Masu aikin gaggawa sun ce sun kai dauki ne bayan sun samu rahotanni dake nuna gidaje arba’in sun fadi a fadin Nashville.

Kaza lika, jami’ai sun samar da matsugunnai na wucin gadi ga mutanen da guguwar ta tilasta ma barin gidajensu.

Guguwar ta AU ta auku ne a wani karamin filin jirgin sama na garin da ke yammacin Nashville in ta kashe a kalla mutun biyu..

Mahaukaciyar guguwa ta fara ne a kusa da karamin garin Camden, mai tazarar kilomita 160 yamma da Nashville, inda ta kashe mutum daya.

Masu nazarin siyasa sun ce akwai yiwuwar guguwar ta shafi kada kuri’a a zaben yau a Tennessee, wacce ta ke daya daga cikin jihohi goma sha hudu da za a gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan jam’iyyar ‘yan takarar jam’iyyar Democrat.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG