Masu hasashen yanayi sun ce guguwar ta Laura tana tafe ne da iska mai karfi da kuma ruwan sama kama da bakin kwarya, inda ta ratsa bangaren gabas na tsakiyar Amurka.
Guguwar ta ratsa gabar tekun Mexico a farkon wannan makon, ta mika daga mataki na daya har ya zuwa mataki na 4 a cikin kasa da sa’o’i 24. Masu hasashen yanayi sun auna karfin iskar da cewa tana cin nisan zangon kilomita 240 a cikin sa’a daya.
A yayin da Laura ta daki kudancin Louisiana da safiyar Alhamis, hukumar kula da guguwa ta Amurka ta yi hasashen samun hadari sosai, yayin da rahoton farko ya nuna cewa tsananin guguwar bai kai yadda aka yi tsammani ba.
Lamarin ya yi sanadiyyar lalata gine-gine, ya kakkarya itatuwa, ya kuma yi sanadiyyar rashin wutar lantarki a jihar. Hukumar ta MDD ta ce guguwar ta Laura, ta soma mikawa zuwa yankin Caribbean a makon jiya, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 20, mafi akasari a Haiti.
Da yake bayani daga shelkwatar MDD a Geneva, mai Magana da yawun hukumar kula da yanayi ta duniya Clare Nullis, ya ce guguwar ta Laura ta sami karin karfi wanda ake amfani da shi wajen auna tsananin hadari da tsawon lokacin da ya dauka, fiye da na hadari 4 da aka yi a watan Agusta.
Nullis ya ce har yanzu da sauran aiki a wannan shekara. Kakar guguwar tekun Atalantika ta soma ne a watan Yuni, za ta kuma karkare a watan Nuwamba.
Facebook Forum