Hukumar kula da matsananciyar guguwa ta fadi cewa tun da guguwar ta shiga cikin birnin ta haddasa rashin wutar lantarki ga dubunnen gidaje da wuraren kasuwanci.
Tun da farko, Isaias ta sauka a bakin tekun Isle Beach tare da iska mai gudun mil 85 cikin sa’a guda wato kilo mita 140 cikin sa’a guda da karfe 11 na daren jiya.
Masu hasashen yanayi sun ce North Carolina da South Carolina da ma wasu jihohi dake nahiyar zasu sami mamakon ruwan sama.
Jihohin dake kan hanyar Isaias zasu fuskanci ruwan sama mai yawan gake da zai haddasa ambaliya a yau har zuwa dare.
Facebook Forum