Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyautar Bishiya Daga Faransa Zuwa Amuka Ta Bace A Cikin Fadar Whihe House


A ranar lititin da ta gabata 23 ga watan Afrilun 2018 ne ‘yan jaridu suka dauki hoton shugaban kasar Amurka Donald J. Trump tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron, a inda matansu suka mara musu baya wajen dasa wata bishiyar da ke nuna kyakyawar danganta tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Faransa Macron shi ya kawo wa na Amurka kyautar bishiyar, wacce aka saro reshenta daga uwar bishiyar a wani yanki da aka taba gwabza yakin da kasashen biyu suka farwa kasar Jamus lokacin yakin duniya na daya, wanda sojojin Amurka sama da 2,000 suka rasa rayukansu.

Amma sai ga abin al'ajabi, a yau an wayi gari a cikin fadar shugaban kasar ta "White House" an nemi bishiyar kosama ko kasa sannan babu wani labari har ya zuwa yanzu, sannan jami’an fadar shugaban kasar Amurka ta White House ba su ce komai dangane da bacewar bishiyar ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG