WASHINGTON D C —
Ms. Kate, matar yariman Birtaniya William, ta haifi ɗa namiji a yau. Yaron¸wanda shine dan su na uku, an haife shi da nauyin kilo 3.8.
Fadar masarautar Ingila ta Buckingham ta ce tuni aka sanar da "Sarauniyar Ingila, da Yariman Edinburgh, da yariman Wales, da gimbiyar Cornwall, da Yarima Harry da sauran ‘yan uwan iyayen kuma sun yi farin ciki da labarin,” inda sanarwar ta kara da cewa “gimbiyar da ɗanta suna lafiya."
Yarima William da Kate sun yi aure tun a shekarar 2011. Suna da 'ya'ya biyu: Yarima George mai shekaru 4, da kuma Gimbiya Charlotte, wacce zata cika shekaru uku a mako mai zuwa.
Facebook Forum