Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimiyya Da Fasaha Na Shanawa A Kasuwar Kwalliya


Nesa ta matso kusa, mutun yayi tunanin yana sanye da na’urar kwamfuta a jikin shi, wani zai ce ai bazai taba sabuwa ba, wai bindiga a ruwa. Lallai a wannan karnin na 21, hakan yayuwu har an manta.

A duk lokacin da aka kira mutun a waya, rigar zatayi motsi, kana tayi wuta dan shaida maka cewar ana kiranka, rigar dai an dinka ta ne da wani irin zare da ke dauke da wasu sinadarai da suke hada wayar mutun da riga. Rigar kudinta ya fara daga dalar Amurka $350, dai da naira dubu dari da talatin.

Mr. Ivan Poupyrev, na kamfanin Google, ya bayyanar da cewar sunyi hadin gwiwa da kamfanin dinka kaya na Levi’s, don samar da rigar zamani da mutun baya bukatar rike wayar shi, ko kuma amfani da wayar ta wurare da dama, kamar yadda za’ayi amfani da wayar wajen tafiya mai nuna hanya na manhajar GPS.

Haka idan mutun ya hada rigar da tsarin Bluethooth zai iya sauraren wakoki da suke cikin wayar shi, ko mutun ya hada da runbun ajiyar bayanai na bayyane wanda akayi ma suna “snap tag”

Rigar zata ba mutun damar amfani da wayar shi cikin natsuwa da jin dadi, batare da mutun ya kauda idon shi akan titi ba, ko kan wani abu da ya keyi wanda hakan zai iya haddasa wata matsala cikin gaggawa.

Ita dai rigar itace tashin farko na samar da kayan zamani, don kuwa za’a kaddamar da takalmin zamani, da jakar zamani, haka ma da wandon zamani wanda duk za’a yi musu tsarin amfani da nau’rar kwamfuta mai kwakwalwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG