Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Google Zai Kaddamar Da Sabon Tsarin Sakon Gaggawa


Kamfanin Google ya kammala duk wasu shirye-shirye don kaddamar da sabon tsarin aika sakon gaggawa, da zai maye gurbin tsohon tsarin aika sakon gaggawa ga masu amfani da wayoyin Android.

Sabon tsarin yana kunshe da wasu kayatattun fasali, wanda mutane zasu iya aikawa da sako ga mutane da yawa a lokaci daya “group text” haka da damar aika sakon bidiyo, kana mutun zai iya gani idan abokin maganar shi yana kokarin rubuto mishi sako.

Haka kuma sabon tsarin zai ba mutane damar ganin ko an karanta sakon su da suka aika ga wani ko wasu, mutun zai iya hada tsarin sakon gaggawar shi na text da na sako asusun email.

Sabon tsarin dai ya dade da aka kirkire shi, amma za’a fara amfani da shi akan wayoyin android. Tsarin aika sakon gaggawa nada tsohon tarihi tun a shekarar 1990, wanda mutane kan iya aika sako dake dauke da harrufa 160.

Amma sabon tsarin na wannan zamanin bashi da adaddin abun da mutun zai iya aikawa, kana yana ba mutane damar daura hotuna, bidiyo da ma wasu abubuwa masu kayatarwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG