Taron likitoci 11 na asibitin koyarwa a Jami’ar John Hopkins, dake jihar Maryland a kasar Amurka, sun gudanar da gagarumin aikin dashen gaba da gwaiwa, a karon farko a fadin tarihin kowane nau’in dashe a jikin dan’adam a duniya.
An cire gaban wani mamaci, da aka dasama wani tsohon sojan Amurka, wanda ya gamu da wani hadari, da yayi sanadiyar lalacewar mazakutar sa, biyo bayan taka wani gurneti da yayi lokacin aikin samar da zaman lafiya a kasar Afghanistan.
Likitocin sun kwashe kimanin awowi goma sha hudu 14, wajen gudanar da dashen, inda aka cire gaban wani mutun, aka dasa a karon farko da aka gudanar da irin wannan aikin a tarihin duniya.
Likitocin sun bayyana cewar akwai tabbacin cewar tsohon sojan zai samu lafiya, da kuma fatar dashen sabon mazakutar ta shi, zata bashi damar morema rayuwa a gaba.
Jim kadan bayan kammala aikin dashen mazakutar ga tsohon sojan, matashin ya bayyana cewar, ya fara jin jikin sa ya dawo kamar da, ya kara da cewar, yana fatar abubuwan da likitocin suka ce ya tabbata, don kara samun lafiya da morema rayuwar a duk lokacin da bukatar hakan ta zo, musamman a dai-dai lokacin ganawa da iyalan sa.
Facebook Forum