Musulmi matafiya da wani lokaci ke neman wurin yin salla yanzu zasu iya duba wayarsu ta hannu, mai kwakwalwa da ake kira smart phone da turanci don neman taimako. Yanzu akwai wata manhaja ta waya da ake kira Islamic GPS da turanci, dake nuna masallatai a fadin duniya.
Musulmai dake so su yi salla a wani wuri da ba su sani ba, manhajar Islamic GPS zata iya nuna masu masallaci mafi kusa.
Ikbal Hussain, wanda ke zama a birnin London, shine ya kirkiro manhajar a lokacin da ya kai ziyara Istanbul, dake Turkiyya.
Ikbal ya ce lokacin da ya je Istanbul, ya nemi wurin da zai yi salla, amma saboda kasancewarsa bako, sai abin ya zama da wahala, kuma saboda matsalar bambancin yare, ya dauke shi lokaci mai tsawo kafin ya gano masallaci. A wannan lokacin ne na yi tunini don me ya sa ba zan kirkiro wata manhajar da zata taimaka ba? a cewar Ikbal.
Yanzu haka dai mutane kusan 50,000 ke amfani da manhajar Islamic GPS, yawancinsu daga Indonesia, da Amurka da Kuma Burtaniya.
Facebook Forum