Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Mutun-mutumi Zai Maye Gurbin Teburin Mai Shayi


Kusan ana iya cewa kowace kasa, al’ada da kabila nada tarihin yadda suke hadawa da shan shayin kofi, ya zuwa yanzu wani kamfanin jihar Texas a kasar Amurka, ya kawo sauki ga mutane, inda ya kirkiri wani mutun-mutumi mai hada shayin kofi, a dai-dai lokutan da mutane ke bukatar shi.

Mutun-mutumin na la’akari da irin yadda mutum yake son dandannon kofin shi da kuma a wane lokaci na rana mutum yake sha, don hada shi da zubawa a kofi dai-dai shan duk wani ma’abocin shan kofi.

A cewar wata mata Wendy Cummings, wannan wani abin sha’awa ne, domin kuwa wannan shine karon farko da ta fara ganin wannan mutun-mutumin da dake hada wa mutane shayi yadda suke bukatar shi.

Kuma zai taimaka wajen rage kashe kudi da mutane ma’abota shan kofi kanyi, ta kara da cewar hakan zai taimaka matuka wajen ganin anyi dai-daito wajen hada shayin kofi a duniya baki daya.

Wannan sabon mutun-mutumin zai taimaka wajen kawo saukin hada shayin kofi cikin sauki da gaggawa, kana za’a dinga samun kofi mafi inganci da nagarta, don mutun-mutumin zai auna duk sauran mahadin kayan shayin kofi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG