A bayan jin bahasi daga al’ummomin, shugaban kwamitin Alhaji Tanimu Turaki ministan ayyukan musamman na Najeriya ya gana da manema labarai inda ya bayyana abinda kwamitin yake yi.
Yace suna tattaunawa da wadanda suke waje da kuma wadanda suke hannun hukuma. Bisa ga cewarshi, suna sane da cewa, kawunan ‘yan kungiyar ya rarrabu sai dai da dama suna goyon bayan sulhu abinda yace zai dauki lokaci kafin a sami masalaha.
Shugaban kwamitin ya kuma yaba goyon bayan da jama’a ke ba kwamitin ta wajen bada bayanai da hadin kai kasancewa kowa ya gaji da abubuwan dake faruwa da yake ayyukan ta’addanci sabon abu ne a kasar. Yace gyara yana daukar lokaci sabili da haka ake bukatar jama’a su kara hakuri su kuma ci gaba da bada hadin kai da goyon bayan yayinda suke ci gaba da addu’oi.
Shugabannin addini da kwamitin ya gana da su, sun bada shawara cewa, gwamnati ta tabbata an yi adalci a zabukan da za a yi nan gaba a dukan matakai domin bisa ga cewarsu, samar da shugabannin da al’umma bata so yana haifar da rashin zaman lafiya.
Shugabannin addinan sun kuma bada shawarar daukar matakan sasanta bangarorin da suka sami sabani. Suka kuma jadada bukatar aiwatar da rahotanni da kuma shawarwarin kwamitoci domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Wakilin Sashen Hausa Abdulwahab Mohammed ya aiko da rahoton.