Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Taimaka Wajen Horas Da Sojojin Najeriya


Bindigogin sojojin Najeriya lokacin da suek shirin tashi zuwa aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali, daga filin jirgin saman Kaduna, arewacin Najeriya
Bindigogin sojojin Najeriya lokacin da suek shirin tashi zuwa aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali, daga filin jirgin saman Kaduna, arewacin Najeriya

Horaswar zata hada da sojoji da sauran sassan tsaron Najeriya ta yadda zasu iya takalar matsalolin tsaro kamar irinta kungiyar Boko Haram

Amurka ta bayar da sanarwa jiya laraba cewa zata bayar da karin horaswa ga sojoji da sauran hukumomin tsaron Najeriya, domin fuskantar matsalolin tsaron da kasar take fama da su, musamman ma daga kungiyar nan ta Boko Haram.

A makon da ya shige ne gwamnatin ta Amurka ta yi alkawarin duba yiwuwar bayar da irin wannan gudumawa a tattaunawar da karamar sakatriyar harkokin wajen Amurka mai kula da al'amuran siyasa, Wendy Sherman, ta yi da manyan kusoshin Najeriya lokacin taron Hukumar Kasa da Kasa ta Amurka da Najeriya da aka gudanar a Abuja.

Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja, ya bayar da sanarwar dake cewa takalar tsageranci a Najeriya, na bukatar sanya hannun dukkan hukumomi da bangarorin kasar, ta yadda kowane sashe na Najeriya zai san ana yi da shi.

Sanarwar ta ambaci karamar sakatariya Sherman tana fadin cewa "ana bukatar basira ta dukkan al'ummar Najeriya wajen kalubalantar irin batutuwan dake addabar kasar."

A watan Mayu ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa a yankin arewa maso gabashin kasar domin kalubalantar barazanar kungiyar Boko Haram. Tun daga lokacin, an samu raguwar hare-haren da kungiyar ke kaiwa sosai a fadin arewacin kasar.
XS
SM
MD
LG