Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojin Mayakan Sama Sun Soma Shawagi Kan Sansanonin Boko Haram


Sojoji
Sojoji

Sojin mayakan sama sun soma shawagi kan wuraren da ake zato sansanonin 'yan Boko Haram ne.

Gwamantin Nijeriya a karo na farko ta fara anfani da sojin mayakan sama wurin gano sansanonin 'yan kungiyar Boko Haram a wani sabon mataki na kokarin dakile tashin tashinar da yaki ci yaki cinyewa.

An ajiye dakarun mayakan saman ne a jihar Adamawa daga inda suke tashi suna kai farmaki ma 'yan ta'adan Boko Haram masu tayarda kayar baya. A zantawarsa da Muryar Amurka kwamanadan mayakan Babban Hafsan Air-vice Marshall Alex Bade ya ce tuni sun fara shawagi kan duk iyakokin Nijeriya da kasashe dake makwaftaka da mu domin kada a yiwa kasar bazata. Shi dai babban hafsan ya je jihar Adamawa ne domin ganin da idanunsa yadda ake gudanar da dokar ta baci a jihohin Adamawa, Borno, da Yobe.

Wani mai magana ya yawun sojin saman ya ce idan sojojin kasa sun sanardasu inda Boko Haram suke zasu bi su zuba masu bama-bamai daga sama. Ya rage ma sojojin kasa su bi sawu. Zargin cewa da manufar siyasa aka kafa dokar ta baci a Adamawa shi hafsan wanda dan Adamawa ne ya ambaci wurare da dama da 'yan Boko Haram suka kai hari a jihar. Dan majalisar tarayya daga jihar Haske Hananiya ya ce hakuri mutanen jihar zasu yi domin sun zauna da mahukunta a Abuja kafin kakaba dokar. Ya ce tun da an dena jin sata da makami to nan da dan lokaci kadan abubuwa zasu daidaita.

A wata sabuwa kuma Lamidon Adamawa Dr. Barkindo Aliyu Mustapha na yunkurin sasanta gaggan 'yan siyasar Adamawa dake rikici da juna lamarin da ya kusa durkusar da jihar. Su ma talakawan jihar suna kokawa yayin da suke cewa rayuwarsu na cikin kunci sanadiyar rikicin siyasar da ya addabi jiharsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00
Shiga Kai Tsaye
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG