Domin tabbatar da gaskiyar maganar abokin aiki Sahabo Iamam Aliyu ya zanta da Manjo Yahaya Shinku mai murabus. Ya ce shi ma haka ya ji ana cewa yayin da dakarun tsaro suka fafata da kungiyar watakila lokacin ya samu rauni amma ya mutu wurin jinya.
Ko menene ma ya faru ya kamata a duba idan haka ne, mutuwarsa zata kawo canji bisa ga abubuwan dake faruwa? Sai dai Manjo Yahaya ya ce a tashi fahimatar ai shugabansu aka kashe da can kafin Shekau. Bayan mutuwar shugaban Mohammed Yusuf menene ya faru? Kungiyar sake samun wani karfi ta yi. Rigin-gimu suka soma karuwa suna ta bijirowa. Idan aka dauki wannan misali to ashe kashe wani shugaban kungiya ba shine zai kaiga samun nasara ba.
Manjo Yahaya ya yi misali da kungiyar Al-Qaida inda ya ce bayan an kashe shugabanta Osama Bin Laden ai basu fasa yin abun da suke yi ba. Maimakon ayyukansu su ragu sai ma dada shirya kai hari suke yi lamarin da ya sa wasu kasashen Turai tare da Amurka suka rufe ofisoshin jakadancinsu.
Ga karin bayani.