WASHINGTON, DC —
Ganin yadda ake kara samun tashe-tashen hankula a baya bayan nan, hukumar sojojin Nijeriya ta kafa wata sabuwar bataliya a kan iyakar Nijeriya da kasar Kamaru a yankin Mubi.
Wakilinmu da ke jihar Adamawa Ibrahim Abdul'aziz ya ce wannan wani sabon yinkuri ne na kara daura damara a fafatawar da ake yi da kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lid Daawati wal Jihad ko Boko Haram.
Abdul'aziz ya ruwaito Kwamandan da ke kula da ayyukan soji na musamman a yankin Laftana Kanar Bayade Gurama Martins na jaddada cewa saboda fito na fiton da ake yi da kungiyar Boko Haram aka kafa wannan sabuwar rundunar. Ya ce wannan sabuwar bataliyar za ta kasance karkashin Hafsan Hafsoshin sojojin Nijeriya ne.