WASHINGTON, DC —
Rundunar 'Yan sandan jihar Gombe ta arewacin Nijeriya ta ce hadin gwiwar sojoji da 'yansanda sun kashe wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lid Daawati wal Jihad (da ake wa lakabi da Boko Haram) a unguwar da ake kira Burundi da daren ranar Alhamis.
Wakilinmu na shiyyar Bauchi Abdulwahab Muhammad ya ce kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar Gombe DSP Attajiri ne ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce DSP Attajiri ya fada masa cewa jam'an tsaro sun samu labarin buyar wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne a unguwar ta Burundi sai su ka tafi wurin. Ya ce isar su wurin ke da wuya sai 'yan bindigar su ka bude masu wuta, su kuma su ka mai da martani, wanda ya yi sanadin mutuwar 7 daga cikin 'yan bindigar.
Abdulwahab ya ruwaito wasu mazauna unguwar na tabbatar da aukuwar al'amarin.