To sai a jawabinsa Nasiru Zaharadeen mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro ya ce kafin kafa dokar ta bacin 'yan ta'ada suna kai hari gaba gadi da jefa bama-bamai a wuraren da suka shirya kaiwa. Amma yanzu abubuwa sun lafa yayin da 'yan ta'adan suka koma yin sari ka noke. Ya ce sari ka noke kuma ba a Najeriya kawai ake yin haka ba.Ya yi misali da kasar Ingila a lokacin rigimarta da IRA. ya ce sai da suka yi shekara 28 kafin su shawo kan lamarin.Don haka a kasa kamar Najeriya za'a dauki lokaci kafin a iya shawo kan abubuwan dake faruwa. Dokar ta baci ta kwantarda yawanci tarzomar da ake fama da ita da.
Idan kasar Ingila ta yi shekara 28 kafin ta shawo kan matsala da IRA wato kila Nijeriya na iya daukar shekara 50. Nasiru Zaharadeen baya zaton Najeriya zata dade haka kafin ta cimma nasara. Ya ce yanzu an san inda 'yan Boko Haram suke. An turasu lungu. An kakkabesu daga sansanoninsu kuma ba da dadewa ba za'a gama da su.
Dangane da yin anfani da hanyar bincike irin na da sai Nasiru Zaharadeen ya ce kasa ce mai tasowa kuma ba rana daya za'a dena anfani da tsoffin hanyoyi ba. Gwamnati tana kokarin kara kayan zamani domin inganta yadda ake bincike da tsaro.
Dokar ta baci dai ana janyeta ne bayan wata shida da kafata kamar yadda dokar kasar ta tanada. Nasiru Zaharadeen ya ce shugaban kasa yana dubawa. Haka ma 'yan majalisa suna dubawa kuma suna kai ziyara wuraren da dokar ke aiki. Ya ce ba da dadewa ba wasu 'yan majalisa suka kai ziyara suka kuma dawo da rahotanni masu dadi. Don haka da irin wadannan rahotannin akwai yiwuwar janje dokar kafin karshen wata shida musamman idan an samu zaman lafiya mai dorewa.
Ga karin bayani daga Nasiru Adamu El-Hokaya.