Jam’iyyu da kungiyoyin ‘yan adawan Ivory Coast, sunyi kira da a fito a gudanarda gagaruma, mahaukaciyar zanga-zanga a ranakun Alhamis da Jumu’ar nan masu zuwa don a taru aga bayan bijirarren shugaban kasar da yaki sauka ko bayan an kada shi a zabe, Laurent Gbagbo.
Masu adawa da Mr. Gbagbo suna son ya hannunta ragamar mulki ne ga Alassane Ouattara, mutumen da duk duniya ta amince da cewa shine ya lashe zaben shugaban kasan da aka yi.
Mutanen biyu, kowanne ya kafa gwamnati kishiyar juna, kuma kowanne na da mayakan dake tare da shi. Tuni mutumen da shi Ouattara ya nada PM, G. Soro, yace zai kwace tashar Tv ta kasaer, har ma zai nada mata sabon shugaba, kuma sannan ya shige opishin da aka tanadarewa PM don ya soma gudanarda aikinsa.
A halin yanzu kuma Mr. Ouattara ya umurci Babban Bankin Afrika ta Yamma da cewa ya daina baiwa Mr. Gabgbo kudaden gwamnati. Hedkwatar wannan bankin, wanda kasashen Afrika takwas ke anfani das hi, tana a Senegal ne. Kuma idan bankin ya bi wannan umurnin na Mr. Ouattara to Mr. Gbagbo zai shiga matsala babba don ba zai iya samun kuddin biyan ma’aikatan gwamanti da sojoji albashinsu ba.