Kungiyar IZALA ta kan tara sunayen marayu da ma matan da suka rasa mazajensu domin neman tallafi daga wasu kungiyoyi da mutane dake da niyyar taimakawa, daga bisani kuma, kungiyar ta raba kayan da ta tara kamar yadda tayi jiya a Abuja.
Baicin raba wa marayun kayan tallafin da ta tara kungiyar IZALA ta kan dauki nauyin karatun yara marayun domin kada su shiga yawon gararamba kan tituna.
Alhaji Saidu Musa Yalwa shugaban kwamitin marayu na kungiyar IZALA a birnin Abuja ya lissafa kayan da suka saya da kudi nera miliyan biyu da dubu dari shida.
Shugaban kungiyar IZALA Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana mahimmancin tallafin har ma ga ‘yan gidan yari. A kai kayan tallafi gidan yari a yiwa mutanen ciki nasiha sai su zama mutanen kirki. Haka kuma zaurawa a taimaka masu, a koya masu sana’a amma kuma a samu masu aurensu domin tausaya masu. Mai mace daya ko biyu ko uku ya yi kokari ya kara daga zaurawan.
Ga karin bayani.