Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar da Majalisar Dinkin Duniya Ta Kebe Domin Tunawa da Matan da Suka Rasa Mazajensu


Wasu mata da yaransu da suka rasa mazajensu a jihar Borno
Wasu mata da yaransu da suka rasa mazajensu a jihar Borno

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, ta kebe domin tunawa da matan da suka rasa mazajensu a duk fadin duniya, kuma rana ce da take da mahimmanci kwarai musamman ga irin matan da suka rasa mazajensu sanadiyar rikicin Boko Haram a jihohi kamar Borno.

Matan da rikicin Boko Haram ya rutsa da mazajensu a jihar Borno yawancinsu sun zama 'yan Rabana ka wadatamu' sakamakon irin halin mugun kunci da suka fada ciki, su da dimbin 'ya'yansu.

Irin wadannan matan sun rasa masu daukan nauyinsu saboda wasunsu an kashe mazajensu tare da 'yanuwansu, lamarin da ya barsu babu masu kula dasu. Wadannan matan da kungiyar Boko Haram ta rutsa da mazajensu an barsu da yara marayu. Basu da dukiya ko wani da zai dauki nauyin karatun 'ya'yansu. Haka ma ci da sha kan zama masu da wahala. Wasu ma da suke gidajen haya akan koresu saboda rashin iya biyan kudin hayan tare da koran 'ya'yansu daga makarantun da suke.

Irin wadannan matan sun zanta da Muryar Amurka a Maiduguri babban birnin jihar Borno, jihar da kungiyar Boko Haram ta fi yiwa barna.Wata mai 'ya'ya marayu goma tace a kofar gidansu aka kashe mijinta. Wata kuma bam da 'yan Boko Haram suka tarwatsa ya kashe nata mijin, ita ma aka barta da 'ya'ya hudu. Tace yayinda take magana ko abincin da zasu ci babu balantana kudin biyan haya ko makarantar yaranta.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG