Uwargidan shugaban, Aisha Buhari, wadda ta samu wakilcin matar gwamnan Borno Hajiya Nana Kashim Shettima tace suna raba kayan ne wa jama'an da karfinsu ya gaza da nakasassu da wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa dasu.
Kawo yanzu sun raba fiye da dubu daya da dari uku ga mutanen dake cikin birnin Maiduguri da suka hada da mata, da maza da tsoffi da ma kananan yara. Hajiya Aisha Buhari tace nauyi ne da ya fada a kansu kuma tilas su tabbatar cewa sun tallafawa irin wadannan mutanen.
Inji matar gwamnan Borno kusan watanni biyar ke nan da matar shugaban kasa ta fara raba kayan tallafi kuma bata daina ba tana cigaba, kuma zata cigaba da yin hakan kamar yadda tayi alkawari.
Wadanda suka samu tallafin sun nuna murnarsu da godiya tare da yiwa matar shugaban kasa Aisha Buhari godiya da addu'ar fatan alheri. Sun kira sauran masu hali su ma su yi tasu hobasan.
Ga karin bayani.