Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Soma Rabawa Jihohin da Rikicin Boko Haram Ya Daidaita Cimaka


Shugaban Najeriya wanda ya aika da cimaka
Shugaban Najeriya wanda ya aika da cimaka

A wani yunkuri na tallafawa al’ummomin jihohin da rikicin Boko Haram yafi shafa,wato jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe,gwamnatin tarayya ta soma raba kayakin cimaka da suka hada da shinkafa,da masara da kuma wasu kayakin masarufi,don magance matsalar cimaka da za’a iya fuskanta.

An kaddamar da wannan tallafin ne a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya,inda aka tura tirela kusan saba’in.

Wannan rabon kayakin abincin dai na zuwa ne,yayin da hukumomin bada agaji da kuma na samar da abinci na majalisar dinkin duniya ke gargadin cewa muddin hukumomi basu taimaka ba,akwai yuwar fuskantar matsalar karancin abinci da ka iya haifar da tamowa,musamman a jihohin da rikicin Boko Haram ya fi shafa,a arewa maso gabashin Najeriya,wato jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe.

To sai dai kuma don fuskantar wannan barazana dake tafe ne,yasa gwamnatin kasar kaddamar da shirin raba kayakin abinci,don a rabawa al’umma,inda a jihar Adamawa gwamnatin tarayyar karkashin ofishin sakataren gwamnatin kasar,BabaChur David Lawan,ta kai hatsin abinci cikin tirela 70.

Da yake mika kayakin tallafin,sakataren gwamnatin tarayyar,wanda hadimin shugaban kasa ta fuskacin ayyuka da tsare tsare,Hon. Ibrahim Bapetel Hassan,ya wakilce shi yace burin gwamnatin kasar ne na ganin an sharewa al’ummun wadannan jihohi hawayensu,musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.

Da yake karban kayakin tallafin,mukaddashin gwamnan jihar Adamawan,Hon.Martins Babale,ya bayyana kokarin da gwamnatin jihar ke yi a yanzu,musamman ga al’ummomin dake komawa yankunansu da aka kwato.

Sau tari ma dai, jama’a kan koka ne da cewa irin wannan taimako bai kaiwa gare su. Mr Cletus Dallatu na cikin wadanda suka karbi kayakin a madadin jama’an karamar hukumarsa yace zasu yi adalci wajen raba kayakin.

Kawo yanzu,dubban rayuka ne dai suka salwanta sanadiyar rikicin Boko Haram,baya ga wanda aka raba da gidaje,ko da yake an fara komawa,to amma kuma da alamun wasu yankunan ba zasu samu damar soma noma a bana ba,da hakan ka iya jawo karancin abinci a cikin al’umma.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG