Wata tawagar likitocin kungiyar da a karon farko ta samu shiga wani sansani dake Bama a jihar Barno, ta gano yara 16 da suke fuskantar matsanancin 'yunwa data kaisu daf da mutuwa, wadanda nan da nan ta mika su ga wata cibiyar jinyar wadanda 'yunwa ta yiwa katutu.
Kungiyar ta fada jiya Laraba cewa, binciken d a ta gudanar ya gano cewa kashi 19 na yara 800 da suke cikin sansanin suna fama da mummunar 'yunwa mai hadarin gaske.
Kungiyar likitocin ta ci gaba da cewa ta kirga kabururruka 1,233, kuma 480 cikin wannan adadi na yara ne, da aka binne su cikin shekarar da ta shige.
Akalla mutane 188 ne suka mutu a sansanin galibi saboda cutar amai da gudawa da kuma 'yunwa daga 23 ga watan Mayu zuwa yau.
Akwai mutane dubu 24, cikinsu akwai yara 15,000, a wannan adadi 4,500 'yan kasa da shekaru biyar ne.