Wasu mata da Muryar Amurka ta yi hira da su kamar su Gambo Suleiman, A’isha Ali da Sutu Nuhu, sun ce mazansu sun bar su da dawainiyar renon yara ga shi kuma babu taimakon da suke samu daga ‘yan uwa ko dangin mazan nasu. Akwai kuma matsalar kyama da talauci da suke fama da su.
Kimani wadannan mata da yara sama da miliyan dari biyu ne, a cewar wasu bayanai da majalisar dinkin duniya ta fitar na bana mai taken ‘Kauda Zaman Kadaici’ na ranar tunawa da matan da suka rasa mazajensu. Mafi yawansu na zaune nahiyar Afrika da Indiya ne ke rayuwa a wani hali mai ban takaici.
A cikin wannan rahoton, wakilinmu Sanusi Adamu ya yi nazarin halin rayuwa da rukunin na wadanan mata suka fada a ciki a sansanin ‘ya gudun hijira na Damare dake jihar Adamawa, ayi sauraro lafiya.