Shaikh Dahiru Usman Bauchi yace duk da yake akwai bukatar a yiwa shugaban kasa addu'a amma fa lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta sake tunane akan dokar da ta hana shigo da abinci ta kan iyakokin kasar.
Yace bayan sun yiwa shugaban kasa addu'a ya gama hutunsa ya dawo lafiya suna koke su mutanen kasa gaba daya cewa an yi matukar matsuwa saboda hana shigo da abinci ta kan iyakokin kasar. Yace idan wadansu ne suka bada shawarar to ba'a ji dadin shawarar ba. Yace akwai sura ta musamman a Kur'ani akan shawara.
Ya cigaba da cewa aikin gwamnati ne ta ji koken jama'a ta kuma yi masu maganin abun da ya damesu. Kusan kashi 75 na al'ummar da suka zabi wannan gwamnatin suna cikin damuwa.Saboda haka ya roki gwamnati ta bude iyakoki ta shigo da abinci kafin lokacin da za'a yi noma a samu cimaka.
Shi ma Shaikh Dr Ahmad Abubakar Gumi cewa ya yi irin halin da aka shiga a kasar na bukatar a kara hakuri. Yace sabon tsarin da aka shigo dashi sai an dauki lokaci kafin a fara ganin alfanunsa. Yace tare da tsanani akwai sauki guda biyu saboda haka mutane su yi hakuri. Allah zai kawo sauki. A yi hakuri da ahuwa da jin tausayin juna.
Ga karin bayani.