WASHINGTON, D. C. - Bayan tattaunawa ta kwanaki biyu, masu taimakawa alkali 12 sun sanar da cewa sun samu Trump da laifi kan dukkan tuhume-tuhume 34 da ya fuskanta.
Bisa tsarin shari’a ana buƙatar haɗin kan dukkan masu taimakawa alkali kafin ayyana mutum a matsayin mai laifi.
Trump ya zurawa alkalan ido yayin da aka kira su don gabatar da matsayar da suka cimma.
Mai shari'a Juan Merchan ya dage yanke hukunci zuwa ranar 11 ga watan Yuli, kwanaki uku gabanin fara babban taron jam'iyyar Republican da ake sa ran zai zabi Trump a matsayin shugaban kasa.
Merchan ya godewa masu taimakwa alkalin bisa hidimar da suka yi. "Babu wanda zai iya sa ku yi duk abin da ba ku so ku yi ba. Zabi naku ne,” in ji Merchan.
Hukuncin ya jefa Amurka cikin wani rudani da ba a saba ba, gabanin zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 5 ga watan Nuwamba, lokacin da Trump, ‘dan takarar jam'iyyar Republican, zai yi kokarin sake neman sabon wa’adi a White House a yunkurinsa na kawar da Shugaba Joe Biden na jam'iyyar Democrat.
Trump mai shekaru 77 ya musanta aikata ba daidai ba kuma ana sa ran zai daukaka karar.
"Wannan abin kunya ne, wannan shari'a ce ta magudi da wani alkali mai cin hanci da rashawa ya yi," Trump ya fadawa manema labarai bayan yanke hukuncin.
"Ainihin hukuncin zai zo ne ranar 5 ga watan Nuwamba daga mutane," in ji Trump, yana mai karawa da cewa: "Ni mutum ne marar laifi."
Trump na fuskantar hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, ko da yake wasu da aka samu da wannan laifin sau da yawa suna samun gajeren hukunce-hukunce ne, tara ko kuma hukuncin je-ka-gyara-halinka.
Daure Trump a gidan yari ba zai hana shi yin kamfen ba, ko ya hau mulki idan ya yi nasara.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna