Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Shugaban Kasa A Amurka Suna Kokarin Jan Ra'ayin Mata Domin Samun Kuru'un Su


Election 2024
Election 2024

Mata masu kada kuri’a sun haura rabin masu zabe a Amurka. Wakilin Muryar Amurka Scott Stearns ya yi nazarin a kan abin da ‘yan takara Joe Biden da Donald Trump su ke yi domin samun kuru’un mata.

Galibi gangamin yakin neman zaben ‘yan takara a kan mata masu kada kuri’a ya maida hankali ne a kan dokokin zubar da ciki da ‘yancin haifuwa.

Amma matan Amurka ba batun zubda ciki kadai ne a gaban su ba kana gangamin yakin neman zaben a tabo abubuwa da dama da suka hada da batun tattalin arziki, kiwon lafiya da kuma batun tafka mugun aiki.

Election 2024 Michigan
Election 2024 Michigan

A jihar Minnesota, Rebecca Jensen mai zabe ta ce shugaba Joe Biden ya cancanci samun sabon wa'adi a kan abin da ta ce ya dauki matakan da suka dace.

“Ina ganin abubuwan da suka shafi muhalli suna da matukar muhimmanci. Ina tsammanin tattalin arziki yana da muhimmanci da kuma kula da lafiya. Ni ma'aikaciyar jinya ce don haka har yanzu ina ganin COVID a wurin aiki akai-akai. Kuma mutane suna ci gaba da cewa mun fita lokacin annoba, mun fita lokacin annoba, amma a gaskiya bamu fita ciki ba. Har yanzu muna tsakiyarsa. Don haka ina tsammanin cewa samun wanda ya yi imani da kimiyya a Fadar White House abu ne mai kyau. "

A jihar Nevada, mai kada kuri’a Julie Benb tana neman Donald Trump ya samu wa’adi na biyu.

"Ya taka rawar gani a fannin tattalin arziki. Bai je yaki ba. Akwai zamantakewa mai kyau. Akwai zaman lafiya. Dukanmu muna aiki. Farashin mai bai da tsada. Ina nufin, ya yi abin a zo a gani. Yana son kasarsa. Mutumin kirki ne. Ya kula da iyalinsa sosai don haka zamu dawo da shi.”

Election 2024
Election 2024

Biden yana neman kuru’un mata masu zabe ne da wani shiri na Fadar White House kan binciken lafiyar mata.

“Ku yi tunanin duk nasarorin da muka samu a fannin kiwon lafiya a dukkan mataki, amma bamu maida hankali kan mata ba. Sai da bincike ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya isa gare ku duka."

Trump ya fadawa wani taron matan Krista masu ra’ayin mazan jiya cewa zai kawo zaman lafiya a Turai.

“Kafin na isa Ofishin Oval a fadar White House, jim kadan bayan zabe na, zan kawo karshen mummunan yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine.”

Election 2024 Super Tuesday
Election 2024 Super Tuesday

Cibiyar kula da harkokin mata da siyasa ta Amurka ta ce mata sun fi maza kada kuri’a a duk zaben shugaban kasar Amurka tun daga shekarar 1980. A takarar su na shekarar 2020, wata kididdiga ta Pew Research ta ce Biden ya lashe zaben mata da kashi 11 a kan Trump.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG