Jiya Talata, jarumar fina-finan batsa, Stormy Daniels, ta yi tozali da tsohon shugaban kasar, Amurka Donald Trump a kotu, inda ta bayyana wa masu taimaka wa alkali yanke hukunci a shari’ar da ake masa a birnin New York cewa ta kwana da shi amma ba don ta na so ba a shekarar 2016, sannan daga baya aka biya ta dala dubu $130,000 domin tayi shiru game da lamarin gabanin tsayawa takara da Trump ya yi cikin nasara a zaben shugaban kasa na 2016.
Stormy Daniels ta ba da shaida ta tsawon sa’o’i game da yadda ta hadu da Trump a gasar shahararru ta kwallon golf ta Lake Tahoe a Nevada, yadda ya gayyace ta zuwa cin abincin dare a dakin otal dinsa, yadda ya nuna ma ta "rashin mutunci da ji da kai," da yadda suka tattauna yiwuwar saka ta a shirinsa na “Celebrity Apprentice,” na raha, sannan suka kwanta a gado na takaitaccen lokacin suka yi mu’amala ta jima’i, abin da shi kuma Trump ya musanta faruwarsa.
Lauyan da ke kare Trump, Todd Blanche ya nemi a ayyana ba'asinta marar cancanta bayan da a wasu lokuta ta yi ta furta kalaman batsa a bayanan da ta yi. Amma alkalin kotun kolin New York, Juan Merchan, yayin da ya ce ya so a ce ba ta fadi wasu kalamanta ba, ya ki amincewa da bukatar (lauyan Trump din).
Dandalin Mu Tattauna