A daidai lokacin da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ke shirin bayyana gaban Majalisar Wakilai saboda matsalar rashin tsaro a fadin kasar, ayyukan ta'addanci da sauran aika aikar rashin imani a Najeriya sai ma abin da ya karu, inda har wasu ke nuna takaicin kasawar gwamnati wajen magance matsalolin, duk kuwa da kururuwar jama’a da kuma girmar ta’asar da ake tafkwa.
A cigaba da wanzuwa da ayyukan ta’addanci ke yi, wasu muggan ‘yan bindiga sun kai hari a wani kauye mai suna Ruggar Lome da ke Karamar Hukumar Yabo a jahar Sakkwato, inda su ka hallaka wani magidanci mai suna Awwal, wanda firgitar da ganin irin danyar kisar gillar da muggan su ka yi masa ta sa matarsa, Aisha nakuda ba shiri da kuma haihuwar bakwaini.
Yayin da matar da jaririnta ke asibiti, inda suke samun kulawa, Kantoman karamar hukumar, Bala Musa Yabo, ya yi takaici wannan lamarin. Ya ce faruwar wannan al’amari a Karamar Hukumar, masifa ce babba, wadda ba su taba tunanin za su ga irinta ba.
Irin wadannan ayyukan ta'addancin suna ci gaba da faruwa ne tun ma ‘yan Najeriya ba su gama jimamin kisar gillar da aka yi wa manoman shinkafa ba a jihar Borno.
Kungiyar mabiya akidar Shi'a ta Najeriya, ta bakin jagoranta a Sakkwato Sidi Maniru Mainasara, ta nuna alhininta akan irin wadannan kashe kashen rashin Imani ciki har da wanda aka yi wa manoma kwanan nan a jahar Borno.
Kungiyar, har wayau, ta nuna mamakin yadda gwamnatin Najeriya ke amfani da jami'an tsaro da kayan aiki a wurin da ba nan ne ake bukatar su ba, maimakon ta yi amfani da su wajen magance matsalar rashin tsaro ganin yadda abin ya yi tsanani.
Watakila bayyanar da Shugaban Najeriya zai yi gaban Majalisar Wakilai ta bude wani sabon babi mai sauya salon tunkarar matsalar rashin tsaro, ko a samu shawo kan lamarin.
Ga Muhammadu Nasir da cikakken rahoton: