Harin wanda aka kai a daren ranar Alhamis ya yi sanadin mutuwar mutun guda a lokacin da ‘yan bindigar su tara suka far wa yankin suka kwashe kayan masu shagunan garin suka arce.
Magajin Garin Allela da ke can tare da askarawan Nijer da ke wannan yankin sun kwarari maharan da suka tsallaka zuwa Najeriya kasancewa, wurin da a ka kai wannan harin ba nesa da iyakar ta Nijar da Najeriya yake ba.
Jama'ar garin na Majiya Zanga sun shiga zaman dardar bayan aukuwar wannan lamari, lura da cewa shi ne na farko da auku a garin nasu.
Wannan shi ya sa Magajin na Allela Malam Salifu Suley ce lalle mutane na cikin tashin hankali a garin na Magajiyar Zanga.
Wadannan garuruwa da ke kan iyaka da Najeriya na fuskantar ire - iren wannan matsalar ta rashin tsaro, inda ko a kwanakin baya wadansu ‘yan bindiga dadi sun sace wani ba'amuruke a garin Massalata da ke Nijar, inda aka tsallaka da shi Najeriya.
Abin da ya janyo musu fushin rundunar soja na musamman na Amurka wadanda suka yi kundunbala suka shiga yankin na Najeriya suka kubutar da ba’amurken.