Ayarin ‘yan sandan sun shiga Sokoto ne bayan bibiyar lambobin wayar da aka yi amfani da su, lokacin garkuwa da dan Amurkan, inda yanzu haka aka kama mutane bakwai a kauyen Dambar Dikko dake karamar hukumar Illela.
Sai dai mutanen da aka kama sun yi korafin cewa bayan da aka kama su, an nemi su biya kudaden beli domin a sake su. Lamarin da ya sa mutanen suka sanar da kungiyar kare yancin bil Adama ta Human Right Watch.
Da suke mayar da martani, ofishin ‘yan sanda na yanki na 10 mai kula da jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara, ya ce yana sane da zuwan ayarin kuma sun yi aikinsu bisa ka’ida. Kakakin rundunar ‘yan sandan Bashir Musa, ya bayyana cewa kudaden da aka karba bana beli bane, an karbi kudaden ne kamar yadda aka saba a duk lokacin da za a ajiye wani da ake tuhuma, kuma an mayar musu da kudadensu.
Yanzu haka dai wasu daga cikin wadanda aka kaman tuni an wuce dasu Abuja, yayin da aka bayar da belin wasu wadanda bincike ya nuna basu da laifi.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.