Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Sun Sake Jaddada Bukatar Gaggauta Raba Kasashe Biyu Tsakanin Isra'ila da Falasdinu


Zauran Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya
Zauran Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, kwanaki bayan da Firai Ministan Isra'ila ya dauki matsaya mai karfi na rashin son batun samar da kasashe biyu.

WASHINGTON, D. C. - Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya shaidawa Kwamitin Sulhun cewa, tilas ne a yi watsi da duk wani kin amincewa da shirin samar da kasashe biyu daga kowanne bangare.

Antonio Guteres
Antonio Guteres

Guterres ya yi tambaya cewa, "Akwai wata mafita banda wannan?" "Yaya za a yi zaman sulhu na kasa-daya-tare da dimbin Falasdinawa a ciki ba tare da'yanci da mutunci ba. Wannan ba zai yiwu ba."

Ana gudanar da babban taron kasashe don tattauna rikicin Gabas ta Tsakiya da aka kwashe shekaru da dama ana yi ne sau hudu a kowace shekara a kwamitin sulhun, wanda ake bude wa dukkan kasashe mambobin kungiyar damar shiga. Sama da kasashe 50 ne suka shirya yin magana, kuma da dama sun aika da ministocin harkokin wajensu.

An dauki sabon matakin gaggawa domin warware rikicin na tsawon makonni 15 tsakanin Isra'ila da Hamas a yankin Zirin Gaza inda ya kashe Falasdinawa sama da 25,000 da 'yan Isra'ila da 'yan kasashen waje 1,200.

Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu - Tel Aviv, Jan. 7, 2024.
Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu - Tel Aviv, Jan. 7, 2024.

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yana neman "cikakken nasara ne kawai" kan Hamas "Na fayyace cewa duk wani shiri a nan gaba, tare da yarjejeniya ko ba tare da yarjejeniya ba, dole ne Isra'ila ta mallaki ikon tsaro a daukacin yankin yammacin kogin Jordan.

Wannan ya zama wani sharadin da ya wajaba,” in ji shi, dangane da filayen da ya hada da yammacin kogin Jordan da Gaza. "Ya ci karo da ka'idar ikon mallaka, amma me za ku iya yi?

Da yake magana da Majalisar a ranar Talata, ministan harkokin wajen Falasdinu Riyad al-Maliki ya yi watsi da wannan maganar, kuma ya ce lokaci ya yi da za a amince da kasar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya

Sergey Lavrov na kasar Rasha
Sergey Lavrov na kasar Rasha

Kasashen Larabawa da na Musulmi da dama sun nuna goyon bayansu ga taron kasa da kasa da za a dauki nauyin wannan batu, kamar yadda Ministan harkokin wajen Rasha ya yi.

Sergey Lavrov ya fadawa Majalisar cewa, “Manufar irin wannan taron ita ce shaida kasar Falasdinu; fito da matakan tabbatar da ingantaccen tsaro ga Isra'ila; da kuma daidaita alakar Isra'ila da dukkan kasashen Larabawa, da ma kasashen Musulmi baki daya,"

Uzra Zeya
Uzra Zeya

Amurka na goyon bayan samar da kasashe biyu a matsayin hanya daya tilo mai dorewa ta zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

"Don cimma wannan buri, al'ummar Isra'ila da Falasdinu, da kuma shugabanninsu, dole ne su yi zabuka masu sarkakiya," in ji Uzra Zeya, karamar Sakatariyar harkokin tsaron farar hula da , dimokuradiyya da 'yancin ‘dan Adam na Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG