Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya Zai Kada Kuri’a Domin Shigar Da Kayan Agaji Gaza


Kwamitin Sulhu Na MDD ya dage dakatar da kada kuria neman kai agaji zuwa Gaza
Kwamitin Sulhu Na MDD ya dage dakatar da kada kuria neman kai agaji zuwa Gaza

Isira’ila ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a ranar Talata tare da ci gaba da kai hari ta kasa akan mayakan Hamas a Zirin Gaza, yayin da Amurka ta hada kawayenta don kare hanyoyin jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya daga ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran a Yemen.

Runudunar Sojin Isira’ila ta fada a ranar Talata cewa sabbin hare-haren na ta sun auna wurarren da Hamas ke amfani da su, kuma sojojin Isira’ila sun lalata wata hanyar karkashin kasa a kudancin Gaza.

Ma’ikatar Lafiya ta Gaza da ke karkashin Hamas ta ce hare-haren Isira’ila sun kashe mutane akalla 20 a Rafah,wani birnin da ke kudanci a kusa da kan iyaka da Masar, inda dubban fararen hula suka tsere.

An dan samu saukin tsinkewar sadarwa da internet a Gaza, inda aka ba da rahotan dawo da ayukan sadarwar kadan a wani bangare na kudancin Gaza.

Katsewar sadarwar da aka fara samu a ranar Alhamis ita ce mafi tsawo tun bayan da aka soma yakin.

A birnin New York na Amurka, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya jinkirta kada kuri’a kan wani kuduri da ke neman a dakatar da fada domin saukaka kai kayan agaji ga al’ummar Gaza masu tsananin bukatar abinci da ruwa da magunguna.

A ranar Litinin ne aka sa ran kada kuri’a, amma aka dage a daidai lokacin da ake tattaunawa kan daftarin, a yayin da Hadaddiyar Daular Larabawa da ta tsara daftarin, ta ke neman goyon bayan kudurin.

Daftarin kudirin da VOA ta sami gani, ya bukaci, bangarorin da ke rikici da su ba da izini, da saukakewa da kuma ba da damar kai agajin gaggawa, cikin aminci da kwanciyar hankali kai tsaye zuwa ga al’ummar Falasdinawa a duk fadin Zirin Gaza.

Haka kuma "yayi kiran da a gaggauta dakatar da kai hare-hare" domin ba da damar shigar ayuka da kayan agaji ba tare da wani tarnaki ba.

Kudurin ya kuma bai wa Majalisar Dinikin Duniya damar sa ido don tabbatar da yanayin jigilar kayan agaji zuwa Gaza ta wuraren shiga da yawa.

Yunkurin amincewa da wani kudurin a majalisar a ranar 8 ga watan Disamba bai sami nasara ba saboda Amurka tayi amfani da karfin hawa kujerar naki da ta ke da shi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG