Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Nada Jami'ar Kula Da Ayukan Jin Kai A Gaza


Sigrid Kaag
Sigrid Kaag

A ranar Talata Majalisar Dinkin Duniya ta nada jami'ar da za ta sa ido kan jigilar kayayyakin jin kai zuwa zirin Gaza, a wani bangare na kudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince da shi a ranar Juma'ar da ta gabata don bunkasa ayukan jin kai.

WASHINGTON, D.C. - Sigrid Kaag, ministar kudi ta kasar Netherlands mai barin gado, za ta kasance babbar jami'a mai kula da ayyukan jin kai da sake gina Gaza daga ranar 8 ga watan Janairu, in ji MDD a cikin wata sanarwa.

Taron MDD akan Gaza
Taron MDD akan Gaza

"A karkashin wannan matsayi, za ta samar da hanyoyi tare da sa ido da kuma tabbatar da jigilar kayan agaji zuwa Gaza," in ji MDD. Har ila yau, za ta kafa "ingantaccen tsari" don hanzarta kai agaji zuwa Gaza ta hanyar kasashen da ba su da hannu a rikicin.

Kaag wacce gogaggiyar jami'ar diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya ce, a baya ta jagoranci tawagar kwararrun masana makamai na kasa-da-kasa da aka dorawa alhakin sa ido kan kawar da tarin sinadarai na Syria.

Kaag
Kaag

A watan Yuli ne ta ba da sanarwar cewa za ta bar aiki da gwamnati saboda karuwar rashin kyakkyawan ga 'yan siyasa a Netherlands.

"Muna sa ran yin aiki kafada-da-kafada da Madam Kaag da ofishin kula da ayuka na Majalisar Dinkin Duniya, kan kokarin kara kaimi da kuma daidaita batun isar da agajin jin kai ga fararen hular Falasdinawa a Gaza," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller a wata rubutacciyar sanarwa da ya fitar.

Matthew Miller
Matthew Miller

Kudirin kwamitin sulhu na ranar Juma'a da ta gabata ya gaza yin kiran a tsagaita bude wuta bayan shafe mako guda ana jinkirin kada kuri'a da kuma tattaunawa mai tsanani don kaucewa kin amincewar Amurka.

Ya yi kiran da a dauki"matakai cikin gaggawa na ba da damar fadada ayyukan jin kai kai tsaye cikin aminci, ba tare da tsangwama ba, da samar da yanayin da za'a dakatar da tashin hankali."

Sojojin Isra’ila
Sojojin Isra’ila

Amurka da Isra'ila na adawa da tsagaita bude wuta, suna ganin haka zai amfani Hamas ne kawai. A maimakon haka Washington ta goyi bayan dakatar da yakin don kare fararen hula da kuma 'yantar da wadanda kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su.

Hukumomin lafiya na Falasdinawa a Gaza da Hamas ke mulki, sun ce kusan mutane 21,000 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, inda ake fargabar an binne wasu a karkashin baraguzan gine-gine. Kusan dukkan mutanen Gaza miliyan 2.3 an kore su daga gidajensu a lokuta da dama.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG