Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya Sun Ce Yaki Ya Isa Haka A Gaza


Zirin Gaza
Zirin Gaza

Wakilan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun yi magana game da wahalhalun da ba za su iya misaltuwa ba, sun kuma bukaci kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, a yayin da suka ziyarci yankin Masar na mashigar Rafah, yankin Falasdinawa da aka yiwa kawanya, wajen shigar da kayan agaji.

Wakilin kasar china a Majalisar Dinkin Duniya, Zhang Jun, da manema labarai suka tambaye shi ko yana da sako ga kasashen da ke adawa da tsagaita wuta a Gaza, ya ce abin "Ya isa haka."

Galibin kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan tsagaita wuta nan take, tsakanin Isra'ila da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da ke iko da Gaza, yayin da mummunan yanayi ke kara ta'azzara ga mazaunan yankin miliyan 2.3.

Amurka da ke marawa Isra'ila baya, a makon da ya gabata ta ki amincewa da bukatar kwamitin sulhu na tsagaita wuta cikin gaggawa, a daidai lokacin da tankokin yaki da sojojin Isra'ila suka kaddamar da farmakin da ya raba mafi yawan al'ummar Gaza da muhallansu tare da kashe sama da mutane 18,000.

Wakilan kwamitin sulhu goma sha biyu ne suka halarci wannan tafiya da Hadaddiyar Daular Larabawa ta shirya, domin kai ziyara Rafah, kwanaki kadan bayan Sakatare Janar Antonio Guterres ya yi gargadin cewa dubunnan mutane a yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya suna cikin yunwa kawai.

Bayan tashi zuwa garin Al-Arish, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta UNRWA ta yi musu bayani kan yanayin Gaza kafin su nufi Rafah mai nisan kilomita 48.

Kafanin dillancin labaru na Reuters ne ya hada wannan rahotan.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG