Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Amurka Ta Bukaci Gwamnonin Jihohin Nigeria Da Su Karfafa Matakan Tsaro


Jakadan Amurka a Najeriya Mr. Stuart Symington
Jakadan Amurka a Najeriya Mr. Stuart Symington

A yayin ziyararsa zuwa Flato mataimakin shugaban ofishin jakadancin Amurka David Young, ya nuna takaicinsa ga irin barnar da aka yi lokacin kashe-kashen da aka yi Barikin Ladi inda ya ga yara da mata da suka tagayyara, ya kuma kira a dauki matakan kawo karshen tashe tashen hankali a kasar.

Amurka ta bukaci gwamnonin jihohin Ngeria da su karfafa matakan tsaro musamman jami'an 'yan sanda wajen basu horo da kayan aiki domin samar da tsaro a kasar.

Mataimakin shugaban ofishin jakadancin Amurka a Nigeria David Young, shine yayi wannan kira, a lokacinda ya kai wata ziyara jihar Flato biyo bayan hare-haren da suka janyo mummunar hasarar rayuka a wasu sassan jihar.

Mr. David Young ya ce ya kai ziyarar ce domin ya fahimci abun dake faruwa, da yadda zamu hada kai mu taimaka wajen hana sake aukuwar lamarin. Mr Young ya ci gaba da cewa, yakamata mu taimakawa wadanda rikicin ya rutsa dasu, tare da samar da sabbin salon tabbatar da zaman lafiya.

Akan abubuwan da ya gane ma idanunsa a wuraren da ya je, Mr. Young ya ce ya ji takaicin abun da ya faru a Barikin Ladi, saboda mazauna yankin sun yi hasara da yawa. A cewarsa ya gana da wasu dake gudun hijira a wata majami'a, kuma abun tausayi ne a ga yara basa makaranta saboda sun gudu domin su tsira da ransu. Basu da abinci. Basu da magani. Basu da bandaki. Ya kara da cewa yanayi ne mai matukar wahala. Mr. Young yace su a ofishin jakadancin Amurka, sun yi Allah wadai da yadda wasu zasu dauki bindigogi da adduna suna kashe mutane.

Mr Young ya yaba da matakan da wasu limaman addinin musulunci biyu suka dauka wajen kare wasu mabiya addinin kirista su 400 daga hallaka. Ya ce sun sadakar da rayuwarsu domin mutane dari hudu su rayu. Mutanen sun tsira sabili da wadannan limaman masu son zaman lafiya.

A cewar Mr. Young Amurka ta bada tallafi da yawa wa kungiyoyin dake aikin samar da zaman lafiya inda ya jaddada muhimmancin zaman tattaunawa da shugabannin al'umma da na addini, da zara sun hango abun da ka iya kaiga tashin hankali.

Mr Young ya ce ya kamata Nigeria ta dukufa wajen aiwatar da doka, samar da 'yan sanda da horas dasu da basu kayan aiki da albashi domin su gudanar da ayyukansu na tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu.

Akan irin tasirin da ziyarar zata yi, Sani Suleiman dake aikin samar da sulhu ya yabawa ofishin jakadancin Amurka da kawo ziyarar wadda yake ganin ta karfafa gwuiwa ce ga shugabannin jihar musamman gwamnan jihar. Shi ko Barrister Yakubu Saleh Bawa, ya ce 'yan Nigeria ne zasu iya kawo karshen bala'in da ya addabi kasar. Ya ce matsalar Nigeria ita ce ta kin gaskiya. Idan mutum ya aikata rashin gaskiya a fito a fada kada a ce jinsin mu daya saboda haka za'a a kare shi.

A saurari rahoton Zainab Babaji

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG