Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kafa Dokar hana fita a kananan hukumomi uku a jihar Plato


 Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalong
Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalong

Bayan rikicin da ya barke a karamar hukumar Barikin Ladi da ya lakume rayuka da dama tare da jikata wasu, yanzu kura ta lafa amma an saka dokar hana fita daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a kananan hukumomi uku

Rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato ta ce ta samu nasarar kwantar da rikicin da ya barke a kauyuka hudu a karamar hukumar Barikin Ladi.

Lahadi aka samu mummunar tashin hankali a wasu kauyuka a sassan karamar hukumar Barikin Ladi inda rahotanni ke cewa an kashe mutane da dama an kuma kone wasu kauyuka.

Kakakin rundunar tsaro ta STF Manjo Umar Adam ya ce komi ya lafa. Tashin hankalin ya faru ne sanadiyar harin da wasu mutane da ba’a san ko su wanene ba suka kai kan wasu kauyuka. Yace ma’aikatansu ne suka ji karar bindiga sai suka je wurin suka kuma tarar da mutanen suka maida martini. Sojinsu sun fi karfinsu sai suka gudu.

Bayan mutanen sun gudu sai kuma sojoji suka ji ana kuwa a wani bangaren. Can ma sojoji sun ruga wurin. Y ace sanadiyar harbe-harben akwai wadanda suka ji ciwo da kuma rayuka da aka rasa. Kakakin y ace kawo yanzu da alkaluman wadanda suka rasu ba.Sojoji na gudanar ci gaba da yin sintiri tare da binciken musabbabin tashin hankalin.

Wani mutum dake yankin yace a Gaskiya an kashe Fulani an kuma kashe ‘yan kabilar Berom. An kashe mutane a Gana Ropp. Haka kuma an kashe wasu a Gindin Akwati. Yanzu haka dai zaman dardar ya kima Barikin Ladi.

Wani Bafullatani ya ce su Fulanin Kanem babu wanda yake karesu. Ya ce an datse hanya, babu inda zasu je.

Wani Reverend Iliya Yunana ya bada shawarar cewa zaman tare nada dadi, to amma tilas a shawo kan wannan lamari. Shi kuma shugaba makiyaya, Danladi Ciroma yayi kira ga kira shugabannin addini su hada kai da shugabannin al’umma, domin a samu zaman lafiya.

Gwamnatin jihar ta jajantawa al’ummar karamar hukumar Barikin Ladi saboda tashin hankalin inda ta jaddada anniyarta na tsaron lafiyar al’ummarta. Ta kuma ja kunne masu kokarin mayarda hannu agogo baya akan zaman lafiyan da aka samu da su daina tada rikici. Haka kuma gwamnati ta bada lambobin da za’a kira da zara wani abu ya faru.

A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG