Alhaji Ibrahim K. Idris, shugaban ‘yan sandan Nigeria ya kafa kwamitin da zai binciki kisan ‘yan sanda bakwai da wasu ‘yan bindiga suka yi a Abuja.
Ya umurci kwararrun ‘yan sandan da zasu gudanar da binciken a karkashin jagorancin Kwamishanan ‘Yan Sanda Bala Ciroma da su gudanar da gaggarumin binciken domin gano ‘yan bindigan da suka bindige ‘yan sanda bakwai a cikin Birnin Abuja a ranar biyu ga wannan wata na Yuli.
Wata sanarwa da hedkwatar ‘yan sandan ta aikawa Sashen Hausa na nuna cewar wadannan ‘yan sanda masu bincike an umurce su da su binciko manufar ‘yan bindigan da suka yi aika aikar, kana su bayyana yadda za’a magance sake aukuwar hakan nan gaba.
Bala Ibrahim mai magana da yawun shugaban ‘yan sandan yana mai cewa babban sifetonsu baya daukan irin binciken da wasa. Duk lokacin da wani abu ya faru yana cewa a gaggauta bincike a yi bincike mai zurfi da zummar shawo kan lamarin a kuma maganceshi ta hanyar kamo masu laifin a gurfanar dasu gaban shari’a.
Bala Ibrahim yace shugaban ‘yan sandan ya gayawa masu binciken su gudanar ta yadda ‘yan Nigeria zasu gamsu.
Masana tsaro irin su Malam Kabiru Adamu yayi maraba laledaukan matakin. To amma sai dai ya ce matsalar ita ce a Nigeria akan yi saurin kafa kwamitin bincike amma da zara sun kammala aikinsu sai aji shiru kamar an shuka dusa, ba’a daukan wani mataki ko yin anfani da sakamakon binciken.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum