Rundunar tsaro ta STF a jihar Plato ta cafke mutane hudu da take zargi da kai hari a Mararrabar Kantoma dake yankin Ropp cikin karamar hukumar Barikin Ladi.
Da asubahin ranar Lahadi wasu mahara suka afkawa kauyen Mararrabar Kantoma suka kashe mutane shida tare da kone wurin ibada da asibiti da kuma wasu gidaje.
Kakakin rundunar tsaro ta STF dake jihar Plateau Manjo Umar Adam yace sun samu nasarar cafke mutanen ne biyo bayan kiran gaggawa da jami’ansu suka samu. Jami’ansu sun yi ta harbe harbe tsakaninsu da maharan a lokacinda suka je kama su. Maharan sun gudu da ‘yan wansu da suka ji ciwo amma sojoji sun samu nasarar kama hudu daga cikinsu. Nan take suka shiga bincike wanda yanzu ya kai ga kama mutane goma sha daya.
Hukumar tsaron ta maida hedkwarta Barikin Ladi saboda a cewar kakakin ta ba zata yiwu suna samun zaman lafiya cikin gari amma ana ci gaba da farma mutane cikin kauyuka. Sun koma Barikin Ladin su tabbatar cewa maharan basu ci gaba da cutar mutanen kauye ba.
A halin da ake ciki yanzu gwamnatin jihar ta Plato ta sassauta dokar hana zirga zirga da ta kafa a kananan hukumomin Riyom, Barikin Ladi da Jos ta Kudu.
Yakubu Datti, kwamishanan yada labarai yace sassaucin ya biyo bayan daidaituwar lamura ne amma dokar zata ci gaba da aiki daga karfe goma na dare zuwa shida na safe.
A saurari rahoton Zainab Babaji
Facebook Forum