Gwamnatin jihar Plato ta hana duk wani gangami ko zanga zanga a duk fadin jihar.
Kwamishanan yada labaran jihar Yakubu Datti ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin hana bata gari yin anfani da gangami suna gallazawa mutanen da basu ci ba basu sha ba.
Kwamishanan yace, zaman lafiyar da suka soma samu suna fatan zai ci gaba saboda haka suka haramta duk wani gangami.
Jami’an tsaro sun sanar da gwamnati cewa wasu suna anfani da gangamin suna aikata aikin asha tare da kawo yamutsi cikin jama’a. Sun roki jama’a su bar yin gangami har zuwa lokacin da aka tabbatar da cikakkiyar kwanciyar hankali.
Yayinda wasu ke ganin hana gangami yanzu mataki ne da ya dace, wasu kuma na ganin wata hanya ce ta tauye hakkin mutanen dake da kwararan dalilai da suke son gwamnati ta sani domin ta share masu hawaye.
Wata da ta yi magana da yawun mata ta ce su kan sanya bakaken kaya su fita yin zanga zanga domin gwamnati ta sauraresu. Tace bai kamata gwamnati ta ji tsoron hakan ba saboda jami’an tsaro na nan su ga yadda zanga zangar ke gudana.
A saurari rahoton Zainab Babaji
Facebook Forum