Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jita-Jitar Harin ’Yan Bindiga Ya Sa Mutane Arcewa A Kasuwannin Jihar Binuwai


Gwamnan Benue Samuel Ortom.
Gwamnan Benue Samuel Ortom.

Rahotanni daga jihar Binuwai sun bayyana cewa, bayan samun labarin yiwuwar ’yan bindiga za su afkawa ‘yan kasuwa a yammacin ranar juma’a mutane sun yi ta tserewa don gujewa fadawa a hannu yan bindigan da abun da ka iya biyo baya.

‘Yan kasuwa da ma sauran al’umma da ke cin babbar kasuwar Markurdi sun yi ta gudu, biyo bayan jin labari da rade-radin cewa ’yan bindiga na shirin kai hari kasuwar a yammacin ranar juma’a.

Yadda labarin ya bazu cikin al’umman garin Markurdi ya haifar da rudani a kusuwar, inda mutane ke cewa rashin daukar ire-iren labarin da muhimmanci a baya ne ya kai ga halaka mutane a yankunan da ke kusa da kasuwar da suka yi ta fama da hare-haren yan bindigan a baya.

Majiyoyi daga birnin Makurdi sun bayyana cewa, masu sana’ar haya da ababen hawa ma sun tsere daga yankin baya ga masu saye da sayarwa, masu cin kasuwa da suka yi ta arcewa a kasuwar da ke babban birnin na Jihar Binuwai.

Wasu shaidun gani da ido sun ce, ’yan kasuwa a kasuwannin Wadata da High Level da ke garin na Markurdi su yi ta shiga suna rufe kantunasu tare da komawa gida saboda gudun abin da ka je ya dawo suna mai cewa, yawaitar hare-hare a kwanakin baya-bayan nan a kan hanyar Makurdi zuwa Naka da ke daura da kasuwar na daga cikin dalilan fargabar.

Karin bayani akan: ’yan bindiga, Jihar Binuwai, Markurdi, ’yan sandan, Nigeria, da Najeriya.

Kazalika, wani ganau ya ce, a hare-haren baya-bayan nan mutane sun yi ta yin watsi da jita-jitar da suka ji kan cewa yan bindiga zasu kai harı lamarin da ya tabbata inda aka yi asarar rayuka da yawa.

Duk kokarin ji ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai kan lamarin ya ci tura saidai wasu kafaffen yadda labarai sun ce, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta ce ba su da labari kan lamarin kuma ba zata iya tabbatarwa ba.

A cikin garin na Makurdi dai, majiyoyi sun bayyana cewam an hango jami’an ’yan sanda da yawa suna sintiri a babbar kasuwar domin tabbatar da tsaro.

XS
SM
MD
LG