Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Kafafen Yada Labarai Za Su Taimaka Wajen Magance Matsalar Tsaro a Afirka


Taron kwararru a fannin aikin jarida a nahiyar Afirka da ke gudana a Kano, Najeriya
Taron kwararru a fannin aikin jarida a nahiyar Afirka da ke gudana a Kano, Najeriya

Yau aka shiga rana ta biyu da fara taron kungiyar Malaman koyar da ilimin aikin Jarida da yada labarai ta Nahiyar Afrika, wato African Council for Communication Education dake gudana a Kano.

Taron ya maida hankali ne akan rawar kafofin labaru wajen magance kalubalen tsaro a kasashen Afrika irin su Najeriya.

Jami’ar Bayero Kano ce ke karbar bakuncin taron na bana wadda ake sa ran gabatar da makalu fiye da 200 daga shehunnan Malamai da kwararru akan ilimin aikin jarida da yada labarai a kwalejojin fasaha da Jami’oin nahiyar Afrika.

Dr Mainasara Yakubu Kurfi, shugaban sashen koyar da ilimin yada labarai da aikin jarida na Jami’ar Bayero ya ce kusan kowa ya san cewa a Najeriya akwai matsaloli na tsaro, su kuma a matsayinsu na masana a harkar sadarwa da aikin jarida, taka rawa ya zama wajibi ta bangaren wayar da kan jama'a.

Sabunta manhajar ilimin sadarwa da aikin jarida domin koyar da dalibai a jami’o’, na daga cikin manyan manufofin wannan kungiya ta malam koyar da ilimin aikin jarida ta Afrika wato, African Council for Communication Education, in ji Farfesa Abdallah Uba Adamu.

Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce jami’ar ta yi fice wajen bincike da horas da dalibai a fannoni daban-daban.

Shehunnan malamai a fannin yada labarai da aikin jarida daga kasashen Afrika daban-daban ne ke halartar taron a fili da kuma ta hanyar fasahar sadarwa ta zamani wato Zoom.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG