Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Matafiya A Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja


‘Yan Bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

‘Yan bindiga.

Rahotanni daga yankunan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da gomman matafiya a loakcin da suka datse babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Akwai rahaotanni masu cin karo da juna dangane da labarin 'yan bindigar da ake zargin sun datse babban titin Kaduna zuwa Abuja, tare da sace wasu matafiya da ba'a bayyana adadinsu ba.

Har kawo yanzu dai babu karin bayani game da aukuwar lamarin, amma majiyoyi daga unguwanni da ke kusa da inda llamarin ya auku sun bayyana cewa da misalin karfe 4.00 na yammacin ranar juma’a 'yan bindiga sun kai hari, tare da datse titin Kaduna zuwa Abuja.

Wasu kafaffen yadda labarai sun ruwaito shaidun gani da ido na cewa, ’yan bindigar sun kai wa matafiyan hari ne kan yankunan daura da kauyen Kare da ke kan babban titin na gwamnatin taraya inda suka yi awon gaba da mutane da ba'a tantance adadinsu ba.

Mazaunan yankin da dama sun shaida wa wasu kafaffen yadda labarai cewa, ‘yan bindigar sun bar motar matafiyan da lamarin ya rutsa da su yashe a gefen titi.

Karin bayani akan: 'yan bindiga, Samuel Aruwan, Twitter, Kaduna, Abuja, Nigeria, da Najeriya.

Haka kuma tsohon dan majalisar dattawan Najeriya a Kaduna, Sanata Shehu Sani, ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

Shehu Sani ya wallafa cewa wani daga cikin matafiyan ya kira shi ta wayar tarho ya sanar da shi cewa ’yan bindiga sun datse hanyar Kaduna zuwa Abuja, tsakanin garin Jere da kauyen Katari da tsakar rana inda suka yi awon gaba da matafiya da dama.

A nasa bangare, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammad Jalige, ya bayyana cewa, sun samu labarin aukuwar lamarin saidai ya zuwa lokacin hada wannan labari, rundunar na zaman jiran karin bayani daga DPO na ’yan sandan yankin.

Ita ma gwamnatin jihar Kaduna a wata sanarwa da kwamishinan lamurran tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fitar, ta ce har yanzu ba ta sami tabbaci da cikakken bayani akan harin ba, amma ta ce za ta sanar da cikakken bayani idan ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Har yanzu dai ba a ji daga ‘yan bindigan da suka aikata wannan aika-aikar ba.

A can baya an dade ana fuskantar ayyukan yan bindiga kan titi Kaduna zuwa Abuja, sai dai a baya-bayan nan an dan samu raguwar hare-haren yan bindingan akan titin, bayan da gwamnati ta tsaurara matakan tsaro.

XS
SM
MD
LG