.
Burin da wannan kawancen yake neman cimma shine na abinda suka kira tsamo jamhuriyar daga cikin halin da gwamnatin da jamhuriya ta bakwai suka saka ta a ciki. Tare da kwato al’ummar ta jamhuriyar Nijar ta hanyar shirya gwaggwarmayar kwato iko ko kuma tankwaso da mahukumtan Nijar din da su dawo daga rakiyar korar fara a daji da suka ce gwamnatin Nijar tana yi yau sama da shekaru biyu da rabi.
Dama dai an jima ana harsashen kulla kawance a tsakanin jam’iyu mafiya karfi a jamhuriyar Nijar tun ranar da jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki a jamhuriyar tayiwa wadansu ‘ya’yan jam’iyun dauk daidai kuma ta sakasu cikin gwamnatin hadin kan kasa da shugaban kasar Issouf Mahammadu ya nada a cikin watan Agustan da ya gabata.
Ga cikakken rahoton da Wakilin Sashen Hausa Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko mana.