A cikin hirarsu da Halima Djimroa, Kassoum Mouctar, shugaban majalisar da’ira birnin Maradi ya bayyana cewa, an tafka ruwa kimanin milimita kusan dari, bayanshi kuma aka yi wani kimanin milimita zuwa hamsin da shida, da arba’in da bakwai wanda ya haddasa barna wanda ya maida unguwar Maza da Jika tamkar korama.
Shugaban Majalisar da’irar birnin Maradin ya bayyana cewa, yanzu haka galibin mutanen wannan unguwa kimanin gidaje dari zuwa dari da hamsin suna zaune a azuzuwan makarantu dake kusa da unguwar.
Shima a nasa bayanin Tijjani Inouwa wani mazaunin Damagaran yace an shafe kimanin sa’a guda ana tafka ruwa a wani lokacin kuma da kankara wanda bisa ga cewarshi, tunda yake bai taba ganin irin wannan ruwan ba.
Kawo yanzu mutune uku suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan, yayinda ake ci gaba da tantance irin asarar da ruwan ya janyo.