A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso yace gwamnatin jihar da Jamhuriyar Nijar sun yi yarjejeniya a rubuce da ta bayyana abinda kowanne bangare zai yi.
Bisa ga cewarshi, za a rika daukar yara dari-dari daga kowanne bangare a shekara. Yace yara daga jihar Kano zasu tafi Nijar su fara koyon faransanci kafin a bude makaranta sun fara iyawa da yake kananan yara ne.
Ministar ilimi ta jamhuriyar Nijar Madam Maryamu Ibrahim wadda ta wakilci shugaban kasar Mahammadu Issouf a wajen bukin da aka yi gidan gwamnatin Kano ta bayyana cewa, wannan shirin ilimantarwar zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen da kuma fahimtar juna tsakanin ‘yan makaranta.