Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Sun Soma Tsokaci Kan Kwamitin Taro


Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.
Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.

Ranar tunawa da samun 'yancin Najeriya shugaban kasar Najeriya ya sanarda kafa wani kwamiti da zai shirya taro game da makomar kasar wanda yanzu lamarin ya jawo cecekuce.

Daya ga watan Oktoba na kowace shekara ita ce ranar da Najeriya ke tunawa da samun 'yanci daga kasar Biritaniya. A wannan ranar ta wannana shekarar shugaban kasar Goodluck Jonathan ya sanarda kafa wani kwamiti da zai shirya taro dangane da makomar kasar.

Kafa kwamitin ya zo ma jama'ar kasar da mamaki abun da ya sa wasu sun soma tsokaci a kai.Wadanda suka fara tsokaci sun hada da 'yan dattawan majalisar kasar da 'yan radun kare hakin bil adama. A nasu ra'ayin abun da shugaban kasar ya yi wata hanya ce ta dauke hankulan mutane daga abubuwan dake faruwa kaman cin hanci da rashawa da rashin aikin yi da ka iya kawo sauyi a rayuwar al'ummar kasar.

Umaru Dahiru dan majalisar dattawa ne daga jihar Sokoto ya ce shugaban kasa nada ikon ya kafa kowane kwamiti ya ga dama to sai dai a ganinsa akwai matsala don haka bai ga yadda kwamitin zai yi tasiri ba. Shugaban kasa ya kafa kwamitin ne sabo da wani dalili da shi kansa ya gani. Wannan shekara ta kusa karewa kuma da zara an shiga sabuwar shekara rikicin siyasa za'a soma yi. Tun kafin ma a shiga sabuwar shekarar rikicin siyasar yanzu ta ishi kasar. Ko sha'anin tsaro kadai wani babban matsala ne da ya addabi kasar.Ban da matsalar tsaro akwai rikicin malaman jami'a da na 'yan kwadago ga kuma na likitoci. Duk wadannan sun isa kasar.Idan da gaske a keyi akwai rahotanni da yawa da ba'a yi anfani da su ba wadanda kuma suna da anfani game da cigaban kasar.

Dan majalisar wakilai daga Kano Mohammed Aliyu Wudil ya ce shi yana gani ruwa ne ya kusa karewa dan kada.Ya ce yaudara ce mai kaman baya ba zani. Shugaban kasar ya ga cewa 'yan Najeriya sun fara baya baya da maganarsa domin an dade bangaren Yarbawa suna kiraye-kiraye a yi taron kasa ya ki kulawa.Amma yanzu tun da ya ga abubuwa su kubuce masa shi yasa ya kirkiro da kwamitin domin ya janye hankalin 'yan Njeriya kan abun da suka sa gaba na bai kamata ya cigaba ba. Abun da ya yi yaudara ce.

Sa'adatu Mahdi sakatariyar kungiyar kare hakin mata ta ce abun da shugaba ya yi daidai ne na son kawo masalaha a tsakanin jama'a to amma idan an fara taron wane tasiri zai yi? Ana neman tasirinta ne a warware abubuwan da suka damu kasar?

Ga rahoton Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG