Jamhuriyar Nijar ta kebe ranar biyu ga watan Yulin kowacce shekara domin yaki da mutuwar mata da kananan yara wajen haihuwa. Bukin da uwargidan shugaban kasa docta Malika Issouf ta jagoranta a birnin Maradi.
A cikin jawabinshi ministan lafiya na kasa mallam Sumaila Tanda ya bayyana cewa, kowacce shekara mata dubu shida ke mutuwa bisa kiddidigar Majalisar Dinkin Duniya domin haka ya kamata mutane su yi hattara a cikin kasa.
Mallam Manzo Zanaidu na hukumar kare lafiya ta jiha ya bayyana abinda yake kawo mace-macen mata wajen haihuwa. Yace mafi yawa, idan ance tana da ciki ko nakuda ta kama ta sai a zauna a cikin gida tunda ita bata da ikon tace zata je asibiti, ko kuma bata da halin da zata je likita, to sau da dama akan bari sai lokaci ya kure, idan aka tashi kuma rashin kyaun hanyoyi yana sawa a dauki lokaci kafin a kai asibiti banda haka kuma karancin likitoci yana sawa idan an kai asibiti ya dauki lokaci kafin a ganta.
Ana amfani da wannan buki domin wayar da kan maza su rika zuwa asibiti domin binciken kansu da iyalansu.
Wani magidanci da ya halarci bukin ya bayyana muhimmancin zuwa asibiti ya kuma yi kira ga magidanta su dauki wannan da muhimmanci idan suna da hali.
Wakilin Sashen Hausa Choibu Mani ne ya hada rahoton.