A wani kokarin neman kara yaukin dangantaka da zumunci tsakanin Najeriya da Nijer, majalisar dokokin jahar Zinder a Jamhuriyar Nijar da ta jahar Kano a Najeriya sun amince za su yi aiki tare wajen samar da dokokin da zasu inganta harakokin su na noma da kasuwanci da ilmi domin ci gaban jama’ar kasashen biyu. Kamar yadda za ku ji karin bayani a ci gaban rahoton da Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana daga Kano:
Majalaisar dokokin Kano, Najeriya da Zinder, jamahuriyar Nijer sun kama hanyar karfafa hulda da dangantaka da juna